IQNA

23:57 - August 22, 2019
Lambar Labari: 3483977
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Isra’ila ta bayar da umarnin rusa wasu gidajen Falastinawa a gabashin birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a jiya gwamnatin Isra’ila ta amince da wani kudiri da aka bagatar mata na rusa wasu gidajen Falastinawaa gabashin birnin, bisa hujjar cewa an gina gidajen ne ba bisa ka’ida ba.

Rahoton ya kara da cewa, tunajiya gwamnatin Isra’ila ta bayar da umarnin rusa wadannan gidaje da yawansu ya kai ashirin, dukkaninsu mallamin Falastinawa ne mazauna unguwar Almatar da ke gabashin birnin Quds.

Shedun gani da ido sun ce tunajiya ne gwamnatin yahudawa ta fara girke manyan motocin Buldoza da nufin fara gudanar da wannan aiki na rusa gidajen Falastinawa.

A cikin lokutan baya-bayan nan Isra’ika ta rusa dubban gidajen Falastinawa a yankunan gabashin birnin Quds, da kuma yankunan yammacin kogin Jordan, bisa hujjar cewa an gina gidajen ne ba bisa izini ba, ko kuma sun saba ma ka’idar gine-gine.

Isra’ila tana rusa gidajen Falastinawa ne tare da gina sabbin matsugunnan yahudawa a wuraren da ta rusa gidajen na Falastinawa.

3836663

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: