IQNA

23:17 - September 05, 2019
Lambar Labari: 3484018
Bangaren siyasa, shugaban kasar Iran ya bayyana cewa daga gobe Juma'a ce za a fara jingine yin aki da wani angaren yarjejeniyar nukiliya a mataki na uku.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaban kasar Iran Dr Hassan Rauhani, a dai-dai lokacin da kasar Iran take daukar mataki na uku dangane da yin watsi da wani bangare na yerjejeniyar nukliyar kasar, bisa mataki-mataki, a jiya da yamma ya bayyana cewa daga gobe Jumma’a Iran zata fara aikwatar da mataki na uku ta yin watsi da wasu yerjejeniyar Nukliyar kasar saboda har yanzu turawa sun kasa ciki alkawuran da suka dauka a cikin yarjejeniyar.

Rauhani ya kara da cewa a halin yanzu turawan suna da wasu kwanaki 60 nan ga don aiwatar da alkawuran da suka dauka a cikin yerjejeniyar, ko kuma Iran ta dauki mataki na gaba, wato mataki na hudu.

A ko wani mataki dai gwamnatin kasar Iran tana warware yerjejeniyar ta dauka a cikin yerjejeniyar nukliyar kasar ne, gwargwadon sabawa alkawurin yerjejeniyar da dayan bangaren suka yi. Har’ila yau, Rauhani ya kara da cewa matakan da kasar Iran take dauka sun da ce da alkawura wadanda suka bayyana cewa a duk lokacin da wani bangaren ya kasa cika alkawarin da ya dauka a cikin yerjejenyar, to dayan bangaren yana iya rage karfin rikon da yakewa yerjejeniyar dai-dai da sabawa alkawuran da aka yi.

Shugaban ya kara da cewa, har yanzun kofa a bude take ta tattaunawa danagne da yadda za’a aiwatar da wannan yerjejeniyar, sannan a duk lokacin da turawan suka cika alkawur 11 da suka dauka a cikin yerjejeniyar, Iran za ta koma kan kanta.

A wannan mataki na ukku wanda za’a fara daga gobe jumma’a dai, kasar Iran zata yi watsi da dukkan alkawuran da ta dauka a yerjejeniyar na gudanar da bincike da kuma bunkasa tataccen sinadarin yuranium.

Don haka daga gobe Iran zata bude kofar bincike da kuma bunkasa sinadarin yuranium, da kuma gashashi gwagwadon bukatarta a ko wani bangare na centarifution da take da su da gaggawa.

Shugaba Rauhani ya bayyana daukar wannan matakin na ukku ne, a jiya da dare, bayan ganawar shuwagabannin bangarorin uku masu tafiyar da al-amuran kasar, shugaban bangaren shari’a wato alkalin alakalan kasar, shugaban bangaren kafa dokoki, wato shugaban majalisar dokokin kasar da kuma shugaban bangaren zartarwa, wato shi shugaban kasa.

Ficewar Amurka daga yerjejeniyar nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015 ne, da kuma maida dukkanin takunkuman da suka shafi yerjejeniyar kan kasar Iran da Amurkan ta yi, a ranar 8 ga watan Maris na shekara ta 2018, har’ila yau da kasawar kasashen turai wajen cika alkawura guda 11 da suka dauka dangane da wannan yerjejeniyar kasar, duk suka taru suka tilastawa Iran daukar matakan da take dauka a kan wannan lamarin.

Banda haka, yakamata ko wa ya sani kan cewa dukkan matakan da kasar Iran take dauke a halin yanzu suna tafiya ye bisa sanya ido na hukumar makamashin Nukliya ta duniya. Sannan babu mataki daga cikin matakan nan ukku wanda ya sabawa ita yerjejeniyar ta shekara ta 2015.

Don haka, har yanzun, Iran tana rike da alkawulanta na yerjejeniyar. Banda haka tana daukar wadannan matakan ne don tilastawa sauran kasashen da suka rattabawa yerjejeniyar hannu luzumtar alkawuransu a cikin yerjejeniyar.

Daga karshe iran za ta dauki mataki na uku ne, duk tare da kokarin da gwamnatin kasar Faransa ta yi na gamsar da ita kan rashin daukar matakin na uku.

Wannan kuma, Saboda ta fahinci cewa kasashen na Turai ba a shirye suke susadaukar da wani abu don cimma alkawuran yerjejeniyar 11 da suke kansu ba. Sannan hatta dalar Amurka biliyon 15 wanda faransa ta yi alkawarin zubawa a fagen kasuwanci da kasar ta Iran sun sami sabani a tsakaninsu, su kasashen na Turai dangane da shi.

 

3840222

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: