IQNA

23:55 - September 07, 2019
1
Lambar Labari: 3484025
Bangaren kasa da kasa, an bude makarantar koyon hardar kur’ani mai tsarki ta Azlaf a yankin Daryush na kasar Moroco.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka bude makarantar koyon hardar kur’ani mai tsarki a yankin Daryush na kasar Moroco, ta Azalaf wadda cibiyar kur’ani ta Badr ta dauki nauyin budewa.

Bayanin ya ce taron bude makarantar ya samu halartar masana da jami’an gwamnati gami da malaman addini da kuma malaman jam’a da sauran masu hannu da shuni, gami da sauran mutanen gari, kamar yadda limamai na masalatai a yankin sun samu halarta.

Babbar manufar kafa wanann makaranta dai itace horar da matasa karatu da hardar kur’ani mai tsarki, wadda kuma tana da alaka ne da mabiya darikar Daryush na kasar morocco.

3840541

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ibrahim
0
0
gaskiya hakan yana da kyau domin hakan shine mafita ga rayuwarmu musulmi allah yataimaka kuma da akwai dama gareni dazan halarci wannan makaranta dan neman ilimi amma babu hali danganeda halin da muke ciki a nigeria
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: