IQNA

22:56 - September 11, 2019
Lambar Labari: 3484039
Bangaren kasa da kasa, an buga wata makala mai taken Imam Hussain (AS) da watan Muharram a birnin Kolombo na Sri Lanka.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa,a  jiya an buga wata makala a jaridu da kuma kafofin sadarwa na kasar Sri  Lanka, wadda wasu musulmi suka rubuta, wadda take yin bayani kan tsayin dakan da Imam Hussain (AS) ya yi a gaban Yazid dan Mu’awiyyah wajen kin yi masa mubaya’a domin kare martabar addinin muslunci.

Bayanin makamalar ya ce, wanann tsayin daka da kuma sadaukarwa ta Imam Hussain (AS) da zuriyar manzon Allah (SAW) da kuma sahabban Imam Hussain, ita ce ta cece addinin muslucni daga gurbacewa, domin da Imam Hussain (AS) ya yi wa Yazid Mubaya’a, to da an rasa gane hakikanin addinin muslucni na gaskiya wanda manzon Allah ya zo da shi.

3841416

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: