IQNA

23:37 - September 16, 2019
Lambar Labari: 3484055
Bangaren siyasa, Msawi ya ce; zargin Iran da hannu a harin da aka kai kan kamfanin Aramco babu wata hujja a kansa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Sayyid Abbas Musawi mai magana da yawun ma’aiakatar harkokin wajen Iran ya mayar da martani kan zargin da Amurka ta yi a kan Iran na cewa tana da hannu a harin da aka kaddamar kan babban kamfanin main a kasar Saudiyya.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai yau a birnin Tehran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, zargin da Amurka ta yi wa kasar Iran babu wani dalili a kansa, kuma hakan yana da alaka ne da siyasar Amurka ta ci gaba da tatsar arzikin kasashen yankin.

Ya ce kasar Yemen tana fuskantar hare-hare tsawon shekaru biyar daga Saudiyya, saboda haka ba a bin mamaki ba ne idan Saudiya ta fuskanci hare-haren ramuwar gayya daga al’ummar kasar Yemen kan abin da take aikatawa a kansu, amma zargin wata kasa mai zaman kanta mai cikakken ‘yancin siyasa da hannu a wannan lamari bai yi daidai da hankali ba.

Ya kara da cewa, wannan ba sabon lamari ba ne ga kasar Iran idan Amurka ta yi irin wannan zargi a kanta, domin kuwa duk abin da ya samu Amurka ko kawayenta a yankin gabas ta tsakiya dama za su dora alhakin hakan ne a kan Iran ba tare da wata hujja ba.

Musawi ya ce Amurka tana tsoratar da kasashen yankin gabas ta tsakiya ne dangane da Iran, domin ta ci gaba da tatsar daruruwan biliyoyin dalolin maidaga gare su da sunan ba su kariya daga barazanar Iran.

 

3842457

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iran ، Saudiyya ، yemen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: