IQNA

22:16 - October 02, 2019
Lambar Labari: 3484110
Bangaren kasa da kasa, Allah ya yi wa Sheikh Ahmad Kamaluddin mataimakin bababn limamin kasar Ghana rasuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne ya yi wa Sheikh Ahmad Kamaluddin mataimakin babban limamin kasar Ghana rasuwa, inda jama’a baki daya suna a cikin alhini.

Shehin malamin dai yana daga cikin amnyan malaman addini masu tasiria  akasar Ghana, ya rasu yana da shekaru 103 a duniya.

Sheikh Ahmad Kamaludin dai ya kasance aboki na kusa ga babban limamin kasar ta Ghana Sheikh sharubutu tun lokacin kuruciyarsu, kuma shi ne mahaifin Sheikh Abubakar Ahmad Kamaluddin shugaban mabiya mazhabar Ahlul bait a kasar.

Jakadan kasar Iran a Ghana Ali Reza Faramarzi yana daga cikin wadanda suke karbar gaisuwa a gidan malamin tare da taya iyalansa alhini.

 

 

3846578

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: