IQNA

23:04 - October 03, 2019
1
Lambar Labari: 3484114
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani wafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta a cikin karni na 19 a Malaysia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jaridar New Street Times cewa, Nur Haiza Nuruddin wani musulmin kasar ne dan shekara 56 ya fanshi wannan kwafin kur’ani daga wani dan kasuwa a shekarar 2003.

Ya ce baya son wannan kwafin ur’ani ya fita daga jihar Terengganu.  kuma an rubuta wannan kwafin kur’ani a tsakanin shekarun 1820 zuwa 1850.

A halin yanzu dai an saka wannan kwafin kur’ani a wani wurin baje kolin kayan tarihi na birnin, inda mutane suk zuwa suna duba shi a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwa na tarihi.

Mutane da dama sun nuna bukatar fansar wanann kur’ani, amma mamallakinsa yaki amincewa da hakan, inda ya fifita a bar shi a matsayin wani abu na tarihi ga al’ummarsa.

3846677

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
MUN GODE
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: