IQNA

22:10 - October 04, 2019
Lambar Labari: 3484118

Gwamnan Najaf: An Kame Wasu Na Hankoron Kashe Malamai A Najaf

Bangaren kasa da kasa, Lui Alyasiri gwamnan Lardin Najaf a Iraki ya bayyana cewa, an kame wasu na shirin cutar da manyan malaman kasara Najaf.

Gwamnan Najaf: An Kame Wasu Na Hankoron Kashe Malamai A Najaf

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Lui Alyasiri gwamnan Lardin Najaf a Iraki ya bayyana cewa, an kame wasu na shirin cutar da manyan malaman kasar a birnin na Najaf.

Gwamnan na najaf ya kara da cewa dukkanin mutanen an kame su a lokacin da suka kutsa kaia  cikin unguwannin tsohowar Najaf, ida dukkanin manyan malaman addini na kasar Iraki suke, kuma mutanen suna da wani mummunan kudiri a kan malaman.

Wannan da an zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin mutanen Iraki suke zanga-zanga a wasu biranan kudancin kasar, suna korafi kan matsalolin rayuwa, musamman matsalolin rashin ayyukan yi a tsakanin matasa.

 

3847139

 

 

 

 

captcha