IQNA

23:48 - October 05, 2019
Lambar Labari: 3484123
Kura ta lafa a birnin bagadaza wasu yankuna da dama bayan tashe-tashen hankulan da suka wakana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, an janye dokar hana zirga-zirga a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki, da ma wasu biranan da aka yi fama rikici kwanaki biyu da suka gabata.

Rahoton ya ce a yau shugaban kasar at Iraki Barham Saleh tare da firayi minister Adel Abdulmahdi sun gudanar da wata tattaunawa danagne da abubuwan da suka wakana, domin daukar matakai na gaba wajen ci gaba da daidaita lamurra a kasar.

A daya bangaren kuma shugaban majalisar dokokin kasar ta Iraki a yau ya gana da wakilan masu gudanar da zanga-zanga, domin tatatunawa kan bukatunsu tare da ‘yan majalisa, tare da tabbatar musu da cewa suna hakkin su yi zanga-zangar lumana domin bayyana korafe-korafensu.

 

3847118

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: