IQNA

23:02 - October 09, 2019
Lambar Labari: 3484135
Bangaren kasa da kasa, an bude bangaren nazari kan yaki da tstsauran ra’ayia  jami’ar Aluyun ta kasar Mauritaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin Bawabah News ya habarta cewa, a jiya Aldah Sidi Umar Talib ministan harkokin addini na Mauritania ya  kaddamar bangaren nazari kan yaki da tstsauran ra’ayia  jami’ar Aluyun ta kasar.

A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa ya bayyana cewa, babbar manufar bude wannan bangare ita ce tabbatar da manufofi na addinin muslucni ga masu nazari.

Ya ce addinin muslucni addini ne na zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban dan adam, da kuma girmama juna da mutunta ra’ayi, ba addini ne na rashin kan gado da shirme ba.

Haka nan kuam ministan ya kara da cewa, ganain yadda wasu suke yin amfani da addini a halin yanzu sakamakon yaduwar akidar takfir masu kafirta musulmi da haifar da rikice-rikice cikin musulmi, ya zama wajibi a bude irin wannan bangare domin yin sahihin nazari kan addini.

Baya ga haka kuma a san yadda za a fuskanci irin wadannan gurbatattun akidu da ba su da asali a cikin addini, wadanda su ne suke kai matasa musulmi zuwa ga shiga kungiyoyin ta’addanci da suka addabi al’umma.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3848626

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، babbar ، wannan ، bangare
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: