IQNA

23:55 - October 17, 2019
Lambar Labari: 3484162
Bangaren kasa da kasa, an cafke wani mutum da ya sace wani kwafin kur’ani mai tsarki a kasar Auzbakistan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wani mutum dan kasar Auzbakistan mazaunin birnin Bukhara, ya tafi da wannan kwafin kur’ani zuwa birnin Fargana domin sayar da shi a kan farashin kudi dalar Amurka dubu 200, amma jami’an tsaro sun kama shi.

Wannan kur’ani dai an rubuta shi ne tun a cikin karni na 16 kimanin shekaru dari biyar da suka gabata, wanda Mukka yusuf Sakhaf wani mai fasahar rubutu ya rubuta.

Ana ajiye da wannan kwafin kur’ani ne a  dakin ajiye kayan tarihi na garin Sarmakand, kuma a cikin karni na 19 ne aka sake gyara tsarin wannan kwafin kur’ani.

 

3850379

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: