IQNA

23:57 - October 17, 2019
Lambar Labari: 3484163
Bangaren kasa da kasa, akwai yara kimanin miliyan daya da suke koyon karatun kur’ani a makarantun allo a Aljeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jaridar Almasa cewa, ministan mai kula da harkokin addini a kasar Aljeriya Yusuf Bilmahdi ya bayyana cewa, a halin yanzu akwai yara kimanin miliyan daya da suke koyon karatun kur’ani a makarantun allo a fadin kasar.

Ministan ya ce tsarin karatun allo abu ne wanda aka gada kaka da kakann a kasar, wanda kuma mutane sun ginu a kansa, a kan haka gwamnati tana bayar da gudunmawarta  awannan bangare domin inganta shi.

Ya ce a halin yanzu akwai tsari na zamani da aka yi wanda makarantun allon suke amfana da shi, inda a kan koyar da yara wasu ilmomi na daban na zamani.

Ministan ya cea  jiya ya bude ata makarantar allo a yankin Diraraiyya da ke kusa da birnin Aljiers, kuma makarantar ta fara da dalibai 450, amma za a iya ara daliban zuwa 500, kuma duk gwamnati ta sanya su cikin sabon tsarin na karatun allo na zamani.

3850413

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: