IQNA

22:32 - October 22, 2019
Lambar Labari: 3484179
Bangaren kasa da kasa, ana shrin fara gudanar da taron kasa da kasa na radiyon kur’ani a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Bawwaba News cewa, a gobe ne ake bude taron kasa da kasa na radiyon kur’ani a Masar karo na biyar.

Muhammad Anwar shugaban radio kur’an Masar ya bayyana cewa, taron zai samu halartar manyan baki daga ciki da wajen kasar Masar, da suka hada hard a babban shehul Azhar Ahmad Tayyib, da kuma ministan ma’aikatar kula da harkokin addini Mukhtar Juma’a, gami da babban malami mai bayar da fatawa na kasar da sauransu.

Baya ga haka kuma akwai baki daga kasashen duniya da za su halarci taron, wanda za a fara daga gobe laraba har zuwa ranar Alhamis, inda za a gabatar da shirye-shirye da dama da suka shafi ci gaban da aka samu ta hanayar yada shirin kur’ani a radiyo.

Wannan taro dai tashar radiyo kur’an masar da kuma hadin gwiwar cibiyar kula da gidajen radiyo da talabijin ta kasashen msuulmi ne dai suka dauki nauyin shirya shi.

Cibiyar kula da gidajen radiyo da talabijin ta kasashen musulmi an kafa ne tun a cikin 1975, a lokacin taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi a birnin Alkahira fadar mulkin kasar ta Masar.

 

3851573

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: