IQNA

22:46 - October 27, 2019
Lambar Labari: 3484196
Bangaren kasa da kasa, Amurka ta sanar da cewa an halaka shugaban kungiyar Daesh Abubakar Baghdadi a Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jami’an ma’aikatar tsaron kasar Amurka Pentagon sun ce Abubakar Baghdadi ya halaka a wani hari da sojojin na Amurka suka kai a maboyarsa a garin Idlib da ke arewa maso gabashin kasar Syria.

Wani babban jami’in Pentagon ya sheda wa jaridar Newsweek ta kasar Amurka cewa, suna da tabbaci kan cewa harin nasu ya yi nasara wajen kashe Abubakar Baghdadi.

Sai dai wasu majiyoyin a ma’aikatar tsaron kasar ta Amurka sun ce, Abubakar Baghdadi shi ne ya kashe kansa da kansa a lokacin da ake kai harin, inda ya saka wata jigidar bama-bamai kuma ya tarwatsa kansa, amma harin ya yi sanadiyyar mutuwar matansa biyu.

A yau ake sa ran shugaban Amurka zai yi wani jawabi kan batun kisan Abubakar Baggdadi.

 

3852821

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: