IQNA

18:10 - November 28, 2019
Lambar Labari: 3484280

Daesh Ta Sake Dawowa A Cikin Tufafin Al’ummar Iraki

Mataimakin shugaban majalisar dokokin Iran kan harkokin kasa da kasa ya bayyana cewa daesh ta sake dawowa Iraki.

Daesh Ta Sake Dawowa A Cikin Tufafin Al’ummar Iraki

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Hussain Amir Abdollahian babban mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Iran kan harkokin kasa da kasa ya bayyana cewa; ‘yan ta’addan daesh sun sake dawowa amma a cikin fararen kaya na al’ummar Iraki.

Ya bayyana hakan ne a cikin shafinsa na twitter jim kadan bayan wani hari da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Najaf.

Ya e a fili yake kan cewa Amurka da Saudiya da kuma Isra’ila ne suke da hannu wajen daukar nauyin dukkanin abin da yake faruwa a Iraki na ta’addanci, amma a wannan karon ‘yan ta’addan da wadannan kasashen suke yin amfani da su sun sake bayyana ne amma a cikin farin kaya.

3860223

 

 

captcha