IQNA

18:21 - November 28, 2019
Lambar Labari: 3484282
Gwamnatin kasar Iran ta kirayi jakadan kasa Norway domin nuna bacin rai kan kone kur’ani da aka yi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta kirayi jakadan kasar Norway dake a birnin Teheran, a yau Laraba, domin nuna bacin ranta kan yadda wani dan kasar ta Norway, ya kona al’kur’ani mai tsarki a birnin Kristiansand.

Jamhuriya musulinci ta Iran, ta nuna bacin ranta sosai dangane da lamarin, wanda ta ce ya bakanta ran al’ummar musulmin duniya, tare kuma da kira ga mahukuntan kasar ta Norway dasu hukunta mutumin, da kuma hana abkuwar hakan a nan gaba.

Iran ta bakin jami’inta mai kula da harkokin arewacin kasashen Turai, ta gargadi kasar ta Norway akan hatsarin dake tattare da irin danyen aiki, wanda zai kan iya tada fitina.

A ranar 16 ga watan Nuwamban ne, Lars Thorsen, jagoran wata kungiyar dake kin jinin wanzuwar musulinci a kasar Norway, yayi yunkurin kona al’kur’ani mai tsarki a binrin Kristiansand.

 

3859865

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iran ، Norway ، jakadan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: