IQNA

Wata Jami’a A Amurka Na Bincike Kan Wani Bidiyon Cin Zarafin Dalibai Musulmi

15:05 - December 05, 2019
Lambar Labari: 3484293
Bangaren kasa da kasa, jami’ar Denver da ke jihar Colorado na bincike kan wani bidiyon cin zarafin dalibai musulmi a jami’ar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin My Met Media ya bayar da rahoton cewa, jami’ar Denver da ke jihar Colorado ta fara gudanar da kan bincike kan wani bidiyon cin zarafin dalibai musulmi wanda aka dauka a cikin jami’ar.

Bidiyon mai tsawon dakikoki 20 ya samu masu kallo kimanin dubu 360 a cikin dan kankanin lokaci, wanda a cikinsa wata daliba take cin zarafin wasu dalibai biyu, daga cikinsu daya na yin salla.

Daya daga cikin daliban musulmi ya bayyana cewa, suna gudanar da salla a wannan wuri tsawon lokaci ba tare da wani ya taba cin zarfinsu ba, kamar yadda kuma hukumomin jami’ar bat aba hana su ba.

3861679

https://iqna.ir/fa/news/3861679

captcha