IQNA

17:20 - December 09, 2019
Lambar Labari: 3484306
Bangaren kasa da kasa, an yaye daliban farko na cibiyar koyon kur’ani mai tsarki da ke Abuja Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafin jaridar Daily Trust cewa, a jiya an kammala bayar da horo na koyon karatun kur’ani mai tsarkia  wannan cibiya ta Laila Dogon Yaro da ke Abuja.

Hajiya Binta Dogon Yaro daya daga cikin wadanda suka halarci wannan horo ta bayyana cewa, wannan cibiya tana gudanar da ayyukanta bisa sahihiyar koyarwa ta musulunci.

Uma daya cikin manufofin cibiyar ita ce fito da hakikanin kyakkyawar fuska ta musulunci, sabanin yadda wasu suke kokarin bata wanann fuska kamar kungiyoyi irin su Boko Haram ko Daesh da makamantan su.

Maryam Baba Muhamad babbar darakta ta cibiyar tace horon ya dauki tsawon watanni takwas.

3862789

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، wasu ، Abuja ، Najeriya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: