Kamfanin dillancin labaran IQNA, mutane da dama ne suka gudanar da gangami da jerin gwanoa birnin Bagadaza na kasar raki, domin nuna rashin aminewa da katsaladan da kasashen waje suke yi a cikin harkokin kasar.
Wannan dai na zwa e sakamakon yadda wasu suke yin afani da jerin gwanon da ake yi ne kasar wajen tayar da hankali da kuma barnata dukiyoyin gwamnati da na jama’a, da nufin cutar kasar a siyasance.
A nasa bangaren shugaban gungun Hikma Sayyid Ammar Hakim ya bayyana cewa, a halin yanzu babu ko daya daga cikin makusantansa da suke da niyyar tsayawa takarar neman kujerar firayi ministan kasar.
Al’ummar Iraki na zargin wasu masu shiga cikin zanga-zangar da cewa an dauki nauyinsu n daga wasu kasashe domin kawai su kawo tashin hankali da yamutsi a kasar kamar dai yadda ake gani.