IQNA

Adadin Musulmi Ya Karu A Majalisar Dokokin Birtaniya

19:16 - December 15, 2019
Lambar Labari: 3484322
Sakamakon zaben ‘yan majalisar dokokin Birtaniya ya nuna cewa musulmi 19 ne suka samu nasara.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, bisa ga sakakon zaben ‘yan majalisar dokokin Birtaniya musulmi 19 ne suka samu nasarar lashe kujeru a majalisar.

A shekara ta 2017 muuslmi 15 ne suka shiga majalisar Birtaniya, inda yanzu adadin ya karu da ashi 20 cikin dari, 15 yan jam’iyyar Labour ne, yayin da sauran kum a’yan jam’iyyar masu ra’yin yan mazan jiya ne.

Wannan ya nuna cewa adadin musulmin da suke shiga majalaisar yana karuwa, inda a 2005 musulmi 4 suka shiga majalisar, a 2010 kuma 8, a 2015 13, a wanann shekara kuma goma sha tara.

A halin yanzu kashi 3 cikin dari na ‘yan majalisar kasar su 650 musulmi ne, inda uma adadin musulmin kasar ya kai kashi 5 cikin dari na dukkanin al’ummar Birtaniya.

A wanann karon akwa ‘yan takara 70 wadanda duk yan asalin Pakistan ne, 20 daga cikinsu yan jam’iyyar conservative ne, 19 kuma yan Labour, sauran kuma daga sauran jam’iyyu.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3864179

 

 

 

captcha