IQNA

19:37 - December 17, 2019
Lambar Labari: 3484326
Ana ci gaba da gudanar da gasar kur’ani mai tsarki a birnin Ajaman tare da halartar makaranta 2137.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, cibiyar ur’ani Hamid Bin Rashed Al-nu’aimi ta sanar da cewa, an fara gasar Ajman wadda za ta ci gaba har zuwa makonni uku a nan gaba.

Wannan gasa dai ana gudanar da ita ne a matsayi na kasar baki daya a hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar makaranta maza 901, sai kuma mata 1236.

An kasa gasar zuwa bangarori daban-daban, tare da yin la’akari da matsayi na shekaru da kuma karatu da harda, kuma wadannan masu gasa duk sun fito ne daga yankunan daban-daban na kasar hadaddiyar daular larabawa.

 

https://iqna.ir/fa/news/3864715

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: