IQNA

21:58 - January 16, 2020
Lambar Labari: 3484420
Bangaren kasa da kasa, za a sake gina wasu dadaddun masallatai a kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, gwamnatin Saudiyya na da shirin sake gyara wasu tsoffin masallatai a yankunan Makkah da kuma Baha, tare da bude su domin yin amfani da su.

Massalatan Jarir Albajali da kuma Sulaiman a garin ta’if, sai kuma masallatan Almalad, Atawila da kuma Zafar a garin Baha, wadanda aka rufe tun shekaru 40 zuwa 60 da suka gabata, za a bude su bayan kamala gyaransu.

Masallacin Jarir bin Bajli wanda ake danganta shi da Jarir bin Abdullah Albajli daya daga cikin sahabban manzon Allah (SAW) na daga cikin muhimman masallatai da za a bude.

Manufar hakan dai ita ce kara samar da wurare na ziyara da bude ido, domin kra samun kudaden shiga ga gwamnati.

 

https://iqna.ir/fa/news/3871802

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: