IQNA

Ministan Kula Da Harkokin Addini A Jordan Ya Ce Masallacin Quds Na Cikin hadari

22:16 - January 18, 2020
Lambar Labari: 3484427
Muhammad Alkhalaya minista mai kula da harkokin addini a Jordan ya bayyana cewa Quds na cikin hadari.

Kafanin dillancin labaran IQNA, Muhammad Khalaya ya bayyana cewa, yadda Isra’ila ta ke tilasta dubban masallata ficewa daga cikin masallar Aqsa tare da hana su yin salla, ya tabbatar da cewa makomar masallacin na cikin hadari.

Ya ce abin takaici ne yadda yahudawa za su hana musulmi yin salla a cikin masallacinsu, wanda a cikinsa manzon Allah (SAW) ya yi mi’iraji.

Ya kara da cewa wannan ba abu ne da musulmi za su yi shiru da bakunansua  kansa ba, domin kuwa wanna ya nuna cewa babbar manufar ita ce addini ba wai ginin masallaci kawai ba.

A jiya Juma’a bayan kammala sallar Asubah, yahudawa sun kori dukkanin msuulmin da suke cikin masallacin, kamar yadda kuam suka hana dubbai gudanar da sallar Juma’a.

 

https://iqna.ir/fa/news/3872327

 

captcha