IQNA

22:31 - January 18, 2020
Lambar Labari: 3484429
Bangaren kasa da kasa, an sanar ad sakamakon gasar kur’ani ta Najeriya da ta gudana a jihar Lagos.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, jaridar Vanguard ta bayyana cewa, an sanar da sakamakon karshe na gasar kur’ani ta kasa karo na 34 da aka gudanar a jihar Lagos da ke Najeriya.

Shugaban majalisar musulmin jihar Lagos Tajuddin Musa ya bayyana cewa, gudanar da wannan gasa ya kara tabbatar da hadin kai da ke tsakanin mabiya addinai a Najeriya.

Inda ya ce gwamna kirista ne ya jagoranci bude wanann gasa, kamar yadda kuma shugaban jami’a wanda kirista ne, shi ne ya samar da wuri da kuam dukkanin abubuwa bukatuwa a lokacin gudana da wannan gasa.

A yayin bude gasar, gwamnan jihar Lagos ya bayyana cewa, dole ne a yi amfani da irin wannan dama wajen kara wayar da kan al’umma hakiaknin koyarwar addinai da aka saukar daga sama, domin kuwa suna yin kira ne zuwa ga zaman lafiya da girmama dan adam da kuma taimakekeniya.

Mutane 359 ne suka halarci wannan gasa, da hakan ya hada da bangaren maza da kuma bangaren mata, a bangaren maza Umar abdulkabir ne ya zo na daya daga Kaduna, sai kuma bangaren mata Diya’atu sani Abdulkadir ce daga Kano ta zo ta daya.

An bayar da kyautuka na motoci ga kowannensu, da kuma kudi naira dubu dari biyu da hamsin.

 

https://iqna.ir/fa/news/3872368

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: