IQNA

20:40 - January 23, 2020
Lambar Labari: 3484441
Ilhan Omar ‘yar majalisar wakilan Amurka ta caccaki gwamnatin Al Saud kan zargin kutse a cikin wayoyin jama’a.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Ilhan Omar ‘yar majalisar wakilan Amurka ta bayyana masarautar Al Saudda cewa, daga kisan yara da mata da kananan yara a Yemen da kashe ‘yan jarida, an koma yin kutse cikin wayoyin mutane.

Ta ce abu mafi muni dangane da abin da masarautar ‘ya’yan take tafkawa shi ne yadda shugaban Amurka yake kare ta ido rufe saboda kudadensu da yake karba.

Jaridar Guardian ce dai ta fara bayar da rahoton cewa, Bin Salman yay i kutse cikin wayar mai kamfanin Amazon Jeff Bezos, wanda kuma shi ne ke da jaridar Washington post.

Majalisar dinkin duniya ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan wannan lamari mai matukar hadari.

 

https://iqna.ir/fa/news/3873735

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Al Saud ، Ilhan Omar ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: