IQNA

Sakon Jagora Ga Taron Kungiyoyin Dalibai Musulmi A Nahiyar Turai
17:33 - January 25, 2020
Lambar Labari: 3484447
Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a cikin sakon nasa ya bayyana cewa, abubuwa da suke faruwa a halin yanzu a duniyar musulmi na nuni da wani sabon canji da ke zuwa ne a nan gaba.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai an jagora ya bayar da sanarwar cewa, an karanta sakon jagora a taron kungiyoyin daliban jami’a musulmi a kasashen turai a birnin Vienna kamar haka:

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai

Dalibai mambobi na kungiyoyin musulmi a jami’oin turai

A wannan shekara a zamanku da ke gudana  a karo na hamsin da hudu, abubuwa da dama sun wakana a cikin kasashen musulmi da suke nuni da gagarumin canji da ake samu a duniyar musulmi.

A jamhuriyar muslunci ta Iran, abubuwan da aka gani a wanann shekara sun hada da shahada, karuwar karfin soji, ci gaba a dukkanin bangarori na ilimi, na addini da kuma na ruwa a bangarori daban-daban, da kuma kara yin tsayin daka wajen kare manufofi juyi, wanda fitowar al’umma ke nuni da hakan, musamman ma matasa, duk wannan na daga cikin abubuwa da suke nuni da gagarumin sauyi da yake tafe a duniyar musulmi.

Da yardar Allah da karfin ikonsa, da wannan ne al’ummar musulmi za ta kai ga samun nasara wajen dawo da martabar addininta a duniya.

Tsarkake zuciya da kuma dogaro da Allah a cikin dukkanin lamurra, shi ne babban sirrin samun nasara a cikin dukkanin lamarran al’ummar msuulmi.

Ina yi muku fatan alhairi da dacewa da taimakon Allah madaukakin sarki.

Wassalamu Alaikum wa rahmatullah

Sayyid Ali Khamenei

23 Janairu 2020

 

https://iqna.ir/fa/news/3873990

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: