IQNA

A jiya miliyoyin mutane a birnin Baghdad ne suka gudanar da zanga-zangar la'antar Amurka, da kuma neman ta fice daga kasar. Muqtada Sadr ne dai ya kirayi zanga-zangar, wadda miliyoyin mutane da suka hada da 'yan siyasa da 'yan gwagwarmaya suka fito.