IQNA

13:24 - January 29, 2020
Lambar Labari: 3484461
Bangaren kasa da kasa, Trump ya sanar da shirinsa da yake kira mu’amalar karni tsakani Falastinawa da Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shugaba Donald Trump, na Amurka ya gabatar da tsarinsa na zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Trump ya bayyana cewa tsarin shi ne mafi dacewa wajen samar da zaman lafiya tsakanin Israila da Palasdinu.

Tsarin ya yi tanadin samar da kasashe biyu Isra’ila da Palasdinu, inda birnin Qudus zai kasance babban birnin Isra’ila, sai dai kuma a daya bangaren ya Ambato cewa gabashin birnin na Qudus zai kasance babban birnin Palasdinawa.

Tuni dai jawabin na Trump, ya jawo muhawara duba da yadda aka kasa sanin hakikanin ina ya dosa, kan matsayin birnin na Qudus, a tsakanin Isra’ila da Palasdinu.

Trump ya kuma mika tayin sasantawa ga Falasdinawa, yana mai cewa Amurka za ta ci gaba da tsayawa a tsakiya don tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Sai dai Falastinawa sun yi watsi da shirin nasa, inda suke bayyana shi da cewa wata sabuwar yaudara ce, da ke nufin halasta mamayar da Isra’ila take yi wa yankunan falastinawa.

 

https://iqna.ir/fa/news/3875000

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Amurka ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: