IQNA

20:59 - February 01, 2020
Lambar Labari: 3484472
An fara bukukuwan zagayowar kwanaki goma na cika shekara 41 da cin nasara juyin juya halin musulinci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a safiyar yau Jagoran Juyin juya halin musulinci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ziyarci hubarren, Imam Khomeini, wanda ya asasa jamhuriya musulinci ta Iran a shekara ta dubu daya da dari tara da saba’in da bakawai.

Sa’annan kuma ya ziyarci makabartun shahidan da suka rasa rayukansu wajen gwagwarmayar data kai ga cin nasara juyin juya halin musulinci a kasar, da wadanda suka mutu a hare haren ta’addanci dama shahidan yakin kallafafen yakin da aka dora wa kasar.

Wadannan bukukuwa za su ci gaba da gudana har zuwa ranar ashirin da biyu ga watan Bahman, wanda ya yi daidai da sha biyu ga watan Fabrairu ranar cimma narara juyin juya halin muslinci na kasar ta Iran.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3875472

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: