IQNA

22:57 - February 08, 2020
Lambar Labari: 3484497
Musulmin kasar Canada na cibiyar (ILEAD) za su gudanar da wani zama mai taken karfafa zamantakewa tsakanin musulmi da sauran al'ummomi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labaran na muslim link ya bayar da bayanin cewa, ana shirin gudanar da babban taron ne na shekara-shekara kamar yadda aka saba.

Bayanin ya ce taken taron na wanann shekara shi ne karfafa zamantakewa tsakanin msuulmi da sauran al'ummomi wadanda ba musulmi, tare da nuna musu kyawawan dabiu irin na addinin musulunci, sabanin abin da suke zato dangane da musulunci.

Raoton ya kara da cewa, daga cikin abubuwan da za a yi nuni a kansua  taron har da yadda ake kafa cibiyoyi na na gudanar da ayyukan alkhari da taimakon marassa galihu, kuma taron zai gudana nea ranar 21 ga watan Maris na wannan shekara ta 2020 da muke ciki.

 

https://iqna.ir/fa/news/3877309

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Canada ، musulmi ، zamantakewa ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: