IQNA

Yunkurin Matasa Na Habbaka Lamurran Da Suka Shafi Kur'ani A Aljeriya

23:35 - February 20, 2020
Lambar Labari: 3484542
Tehran - (IQNA) matasan kasar Aljeriya sun fara aiwatar da wani yunkuri na habbaka lamurran da suka shafi kur'ania kasar.

Shafin tashar aljazeera ya bayar da rahoton cewa, babbar manufar wanann shiri dai ita ce samar da yanayi na habbaka lamurran kur'ani, musammana  bangaren harda da kuma tilawa a tsakanin matasa.

Baya ga haka kuma shirin na da nufin samar da hanyoyi na bayar da horo a kan hukunce-hukunce da suka shafi karatun kur'ani, baya ga haka kuma da koyar da yadda ake yin harda ciki tsari mafi sauki da kuma sauri a lokaci guda.

A bisa ga tsarin, za a samar da manyan cibiyoyi guda 6 a kasar Aljeriya, wadanda za su zama suna da rassa 48 a cikin jihohin kasar, wadanda a cikin yardar Allah a shekaru 10 masu zuwa, za su samar da mahardata kur'ani mai sarki kimanin dubu 15.

Ibrahim La'amuri shi ne shugaban shirin, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun fara gudanar da abubuwa da dama bayan samun amincewar gwamnati da shirin nasu, wanda kuma bisa ga wanann shiri, makaranta kur'ani za su samu takardun shedar karatu da kuma yin amfani da ita wajen koyarwa a makarantun gwamnati da ma wadanda ba na gwamnati ba a kasar.

 

3880122

 

Abubuwan Da Ya Shafa: aljeriya habbaka
captcha