Shafin yada labarai na Republic World ya bayar da rahoton cewa, dubban masu aikin umrah ne suka cika masallacin harami mai alfarma da ke Makka domin gudanar da aikin ibada na umrah.
A daidai lokacin da ake cikin wannan aiki, wasu dubban masu ziyara kuma suna gudanar da ayyukan sa kai wajen taimakawa sauran masu ziyara, da hakan ya hada da share farfajiyar haramin ka’abah, da kuma fesa maganin kashe cututtuka.
Haka nan kuma masu gudanar da aikin umra suna daukar matakai na kare kansu daga kamuwa da cutar tan corona, da hakan ya hada da kiyayae tsafta ta hanyar wanke hannuwa a kowane lokaci, da kuma saka abin da ake rufe hanci da baki da shi.
Saboda yawan amfani da abin rufe hanci da baki, dukkanin wuraren da ake sayar da shi a kusa da harami mai alfarma ya kare baki daya.