IQNA

23:44 - March 05, 2020
Lambar Labari: 3484588
Tehran (IQNA) mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da jingine ayyukan Umrah ga ‘yan kasar saboda matsalar cutar Corona.

Kamfanin dillancin labaran WAS na kasar Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, jami’ai a ma’aikatar harkokin cikin kasar sun sanar da cewa, saboda yaki da yaduwar cutar corona, an dakatar da dukkanin ayyukan Umrah ga ‘yan kasa da baki mazauna kasar.

Jami’an sun sanar da cewa wanann mataki na wucin gadi ne, har zuwa lokacin da za a samu kyautatar lamurra dangane da yaduwar cutar.

Saboda haka a halin yanzu an hana dukkanin mutane kusantar masallacin harami da kuma masallacin manzon Allah.

Kafin wannan lokacin mahukuntan Saudiyya sun sanar da dakatar da bayar da izinin shiga kasar, kamar yadda kuma suka bayyana cewa an samu wani mutum dan kasar dauke da cutar ta corona.

 

3883310

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dauke ، Makka ، masallacin manzo ، Umrah ، matsalar ، mahukunta
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: