Jami'in ya bayyana a cikin shafinsa na twitter cewa, mambobin kwamitin tsaro sun amince da taftarin kudirin da aka gabatar musu kan tattaunawar Amurka da Taliban, da ke neman dakatar da bude wuta a kasar Afghanistan.
Ya ce babbar manufar hakan ita ce samo hanyoyin da za su kawo karshen yaki da tashe-tashen hankula akasar Afghanistan, wanda kuma aiwatar da abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa daga dukkanin bangarorin biyu zai iya haifar da da mai ido ga makomar kasar.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, abu na gaba da yake da muhimamnci a yanzu bayan cimma wannan yarjejeniyar, shi ne mayar da bangarorin gwamnati da Taliban kan teburin tattaunawa, domin samun sulhu da fahimtar juna a tsakaninsu, da hakan zai kawo wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a kasar Afghansitan.
Tuna cikin shekara ta 2001 ce dai Amurka ta kaddamar da hare-harea kasar Afghanistan da sunan kifar da gwamnatin Taliban, wanda kuma tun daga lokacin har zuwa yanzu kasar ba sake sheda zaman lafiya ba.