IQNA

23:58 - March 13, 2020
Lambar Labari: 3484618
Tehran (IQNA) kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China ya bayyana cewa akwai yiwuwar cewa Amurka ce ta shigo da corona a cikin China.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta China ya bayyana akwai zaton cewa Amurka ce ta shigar da cutar Corona a cikin kasa ta China daga garin Wuhan, inda nan ne cutar ta fara yaduwa, a kan haka China tana bukatar bayani dalla-dalla kan wannan batu daga gwamnatin Amurka.

Ya ce daga cikin bayanin da suke bukata har da neman sanin adadin Amurkawa da suka kamu da cutar da kuma lokacin da suka fara kamuwa, da sunan asibitocin da aka kwantar da su.

Ya kara da cewa zato mafi karfi shi ne cewa, sojojin Amurka ne suka yada wannan cutar a cikin kasar China, a kan haka dole ne Amurak ta fito ta yi gwamnatin China bayani ba tare da wasu kauce-kauce ba.

 

3884990

 

Abubuwan Da Ya Shafa: China ، Amurka ، cutar corona ، yahudawa ، sojoji ، Wuhan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: