IQNA

23:58 - March 20, 2020
Lambar Labari: 3484639
Tehran (IQNA) shugaban kasar Tunsia ya bayar umarnin killace kasar baki daya saboda cutar corona.

Tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa shugaban kasar Tunisia ya bukaci da a killace kasar saboda hana yaduwar cutar corona.

Shugaban na Tunisia a cikin wani jawabi da ya gabatar wanda aka watsa kai a gidajen talabijin, ya bayyana cewa dole ne a dauki matakan hana yaduar cutar a cikin kasar.

Ya ce dole n mutane su daina tafiye-tafiye kamar yadda jami’an kiwon lafiya suka bukata.

Yanzu haka dai Tunisia ta rufe masalatai da makarantu da kuma iyakokinta na sama da kasa da ruwa, kuma mutane 54 ne suka kamu da cutar yanzu haka a kasar.

3886683

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shugaban kasar ، Tunisia ، cutar corona ، masallatai ، makarantu ، tafiye-tafiye
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: