IQNA

23:46 - March 27, 2020
Lambar Labari: 3484663
Tehran (IQNA) kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi Allawadai da kakkausar murya kan takunkuman Amurka a kan kasar Iran.

Shafin yada labarai na Sanad lilanba ya bayar da rahoton cewa, kakakin kungiyar Hamas Sami Zuhri ya bayyana cewa, ci gaba da kakaba takunkumin Amurka a kan Iran, cin zarafin ‘yan adam ne.

Ya ce lokaci yay i da Amurka za ta janye takunkumanta na zalunci a kan Iran musamman a wannan lokaci da ake fama da cutar corona a kasar.

Wannan martani na Hamas ya zo ne domin nuna takaici kan yadda Amurka ta kara saka takunkumi a kan mutane 15 da kamfaoni 5 na kasar Iran.

Sabon takunkumin na Amurka ya hada da kamfanonin sufuri, kasuwanci, gine-gine, da kuma wani kamfanin makamashi.

A cikin wanann makon ne kasashe 8 suka aike da wata wasika zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya, da ke kiransa da ya dauki matakin tilasta wa Amurka jane takunkumanta  akan kasar Iran cikin gaggawa.

 

 

3887699

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: