IQNA

23:59 - March 30, 2020
Lambar Labari: 3484669
Tehran (IQNA) jiragen yakin masarautar Al Saud sun kaddamar da munanan hare-hare a kan biranen kasar Yemen a yau.

Jaridar Al-nahar ta kasar Lebanon ta bayar da rahoton cewa, jiragen yakin kawancen Saudiyya sun kaddamar da hare-harea yau a kan yankuna daban-daban a cikin birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen, da ma wasu biranen kasar ta Yemen.

Wannan rahoton ya ce wadannan hare-hare na zuwa ne a daidai lokacin da yakin Saudiyya kan kasar Yemen ya shiga shekara ta shida a jere, ba tare da masarautar Saudiyya ta iya mamaye kasar ta Yemen kamar yadda ta yi zato ba tun daga farko.

A daya bangaren kafofin yada labaran kasar Yemen sun bayar da rahotanni kan cewa, hare-haren na Saudiyya sun yi barna a birnin San’a da kuma biranen Alhudaidah, gami da Sa’adah da Maarib da sauransu

Sai kuma a nasu bangaren dakarun kasar ta Yemen sun sanar da cewa, wadannan hare-hare ba za su wuce ba tare da mayar da mummunan martani na daukar fansa ba kan abin ke faruwa.

 

3888270

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Yemen ، saudiyya ، hare-hare ، kan yankuna ، mutane ، yakin ، kawancen Saudiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: