IQNA

An Dakatar Da Shirin Gasar Kur’ani Ta A Aljeriya Saboda Corona

23:47 - April 12, 2020
Lambar Labari: 3484705
Tehran (IQNA) an dakatar da gasar kur’ani ta duniya da ake gudanarwa kowace shekara  akasar Aljeriya saboda matsalar corona.

Rahotanni dag akasar Aljeriya sun ce, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Aljeriya ta sanar da cewa, saboda matsalar corona da ake fama da ita a kasar da ma kasashne duniya, an dakatar da gudanar da gasar kur’ani ta duniya.

Haka nan kuma sanarwar ta ce baya ga haka ma dukkanin sauran abubuwan da ake gudanarwa  akowace shekara  a cikin watan Ramadan mai alfarma, kam adaga sallolin tarawihi, da tarukan karatun kur’ani na jihohi da sallokin juma’a, duk an dakatar da su.

A kowace shekara dai ana gudanar da gasar kur’ani ta kasa da kasa a kasar Aljeriya, tare da halartar wakilai daga kasashe 60 na duniya.

Ma’aikatar kula da harkokijn addini ta kasar ta bayar da shawar cewa, za  aiya gudanar da wasu lamurran ta hanyar yanar gizo, kamar zaman karatu na larduna da ake gudanarwa.

 

3890947

 

 

 

 

 

captcha