IQNA

Wasu Jiragen Isra’ila Marassa Matuki Sun Keta Hurumin Sararin Samaniyar Beirut

23:48 - April 16, 2020
Lambar Labari: 3484718
Tehran (IQNA) wasu jiragen Isra’ila marassa matuki sun keta hurumin sararin samaniyar birnin Beirut na kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya bayar da rahoton cewa, a jiya wasu jiragen Isra’ila marassa matuki sun keta hurumin sararin samaniyar birnin Beirut na kasar.

Gwamnatin kasar Lebanon ta fitar da bayani a yau inda ta yi Allawadai da kakkausar murya  akan wannan shisshigi na gwamnatin yahudawa  akan kasarta.

Haka nan kuma gwamnatin ta Lebanon ta shirya wata wasika ga babban sakataren majalisar dinkin duniya, inda ta yi karar gwamnatin yahudawan, tare da yin kira da a dauki mataki kan hakan.

3892067

 

 

 

captcha