Shafin yada labarai na khalijonline ya bayar da rahoton cewa, a shirye-shiryen shiga watan azumi na wannan shekara an samar da wani application na wayar salula wanda yake dauke da karatun kur’ani na fitattun makaranta 250 na duniya, wanda za a iya saka wayoyin salula na android ko kuma iOS.
Bayanin ya ce baya ga karatun kur’ani, akwai matanin kur’ani wanda za a iya karantawa da kaloli daban-daban, haka nan kuma za a iya bude hotunan bidiyo na masu karatun kur’ani, ko kuma a sanya sautinsu kadai.
Baya ga haka kuma za a iya sanya tarjama ta kur’ani daga larabci zuwa harsuna 35 na duniya, domin ji ko kuma ganin tarjamar abin da ake karantawa.
A daya bangaren kuma akwai wasu tsare-tsare na koyar da yara karatun kur’ani ko harda ko tafsirin ayoyin kur’ani, kamar yadda kuma akwai kissoshin kur’ani wadanda aka sanya su a cikin sauti domin amfanin yara, kamar yadda kuma addu’oi kimanin 50 wadanda aka ruwaito daga manzon Allah (SAW).