IQNA

Shirye-Shiryen Watan  Ramadan Ta Hanyar Yanar Gizo A Aljeriya

23:56 - April 21, 2020
Lambar Labari: 3484731
Tehran (IQNA) ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya ta sanar da cewa za a gudnar da wasu shirye-shirye a cikin watan ta hanyar yanar gizo ne.

A cikin wani bayani da mai magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin addinin Aljeriya ya fitar a yau, ya bayyana cewa za a gudnar da wasu shirye-shirye a cikin watan ta hanyar yanar gizo ne saboda matsalolin da ake fama das u.

Ya ce har yanzu akwai matsalolin kiwon lafiya da suka shafi corona a kasar, wanda saboda hakan en aka dakatar da abubuwa da dama da hakan ya hada da salloli a masallatai da sauran wuraren taruwar jama’a.

Ya kara da cewa idan wannan halin ya ci gaba har zuwa watan ramada, za a ci gaba da tafiya a haka ne har zuwa lokacin da za a samu saukin lamarin.

 

3893073

 

captcha