Jaridar Al-dastur ta bayar da rahoton cewa, Masar tana fuskantar matsaloli a bangarori daban-daban sakamakon bullar cutar corona, da hakan ya shafi har da bangaren buga littafai da sayar da su.
Umar Adel wakilin madaba’antar Darul Fajr a kasar Masar ya bayyana cewa, tun watanni takwas kafin watan Ramadan suka fara yin cinikin kayayyakin da suke samarwa, amma a hlin yanzu cinikin ua ja baya matuka.
Ya ce kayan da suke samarwa abin da suke sayarwa bai kai kasha goma cikin dari ba, sakamakon matsalar yaduwar corona, ta yadda komai ya tsaya cak, kuma babban abin da suka bugawa da sayarwa awannan lokacin shi ne kur’ani mai tsarki.
Ya kara da cewa, kasashen Rasha, Malaysia da kuma Indonesia su ne kasashen da aka fi sayar da kur’ani da suke bugawa a wannan lokaci, amma shi ma a yanzu bai wuce kasha 10 cikin dari ba.