IQNA

15:46 - May 05, 2020
Lambar Labari: 3484764
Tehran (IQNA) mutane 2,159 ne daga kasashen duniya suka yi rijistar karatun falsafar musulunci a yanar gizo.

Shafin cibiyar muslunci a kasar Afrika ta kudu ya sanar da cewa, bisa sabon tsarin da wannan cibiyar ta bullo da shi a  cikin wanann wata na Ramadan, na karatun falsafar muslunci kai tsaye a  yanar gizo, mutane da dama ne suka yi rijistar sunayensu.

Bayanin ya ce a halin yanzu mutane dubu 2 da 159 suka yi rijista kuma suke bibiyar karatun kai tsaye daga kasashe 38 na duniya, wanda ake gudanarwa a ginin cibiyar na birnin Johannesburg.

Sayyid Abdullah Hussaini shugaban cibiyar ne ke gabatar da karatun kai tsaye daga babban ginin cibiyar da misalign karfe 20:30 na dare agogin kasar Afrika ta kudu.

A cikin shirin dai baya ga karatun da bayani kan falsafar muslucni, an kuma amsa tambayoyin mutane kan mas’aloli daban-daban na addini.

3896710

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: