IQNA

Ayatollah A’arafi: IQNA Na Bayar Da Gudunmawa A Cikin Watan Kur’ani

23:46 - May 09, 2020
Lambar Labari: 3484778
Tehran (IQNA) Shugaban cibiyar ilimi ta Huaza a Iran ya jinjina wa kamfanin dillancin labaran IQNA kan gudnmawar da yake bayarwa a fagenlabaran da suka shafi kur’ani.

Ayatollah Aliredha A’arafi babban daraktan cibiyar ilimi ta Hauza ya taya iqna murnar zagayowar lokacin kafa wanann kamfanin dillancin labarai, ga sakon kamar yadda yake:

Da Suna Allah Madaukaki

Ranar goma sha biyar ga watan Ramadan ran ace da ak akafa kamfanin dillancin labaran kur’ani na kasa da kasa wato iqna, ina mika sakon taya murna ga dukkanin masu aiki a karkashin wannan wuri mai albarka.

Baya mika sakon taya murna da kuma jinjina ga dukkanin jami’ai da ma’aikata na wannan wuri, ina kuma son in jawo hankulansu zuwa wasu abubuwa kamar kamar haka:

1) Su mayar da hanaklai wajen kara fadada ayyukan wannan wuri zuwa kasashen duniya

2) Yi wa duniya bayani kan ci gaban da aka samu ta fuskacin ayyukan kur’ani a Iran da kuma cibiyar ilimi ta hauza.

3) Bayyana abubuwa da suke kunshe a cikin sakon kur’ani mai tsarki zuwa ga al’ummomi na duniya.

4) Fitar da sakon kur’ani na kira zuwa ga hadin kai tsakanin al’ummar musulmi

5) Kokarin samar da hanyar hada fahimta tsakanin bangarori muuslmi a kan koyarwar kur’ani.

Cibiyar Hauza za ta ci gaba da kara bayar da gudunmawa da goyonbaya ga wannan cibiya ta kur’ani mai tsarki.

Aliredha A’arafi

Darakatan Cibiyar Ilimi ta Huaza

7/Mayu/2020

3897455

 

captcha