IQNA

Cibiyoyi 58 A Norway Sun Bukaci A Janye Killacewa Daga Gaza

23:56 - May 09, 2020
Lambar Labari: 3484781
Tehran (IQNA) Kungiyoyi da cibiyoyi 58 ne a kasar Norway suka rattaba hannu kan wata takarda, da a cikin suke yin kira da a kawo karshen killace yankin zirin Gaza da Isra’ila take yi.

 

 

 

Shafin yada labarai na Palestine ya bayar da rahoton cewa, a cikin wata takarda suka rattaba hannu a kanta, kungiyoyi da cibiyoyi 58 a kasar Norway sun bukaci da a kawo karshen killace yankin zirin Gaza da Isra’ila take yi tsawon shekaru masu yawa.

A cikin bayanin, kungiyoyin sun bayyaka killace yankin zirin Gaza a matsayin babban laifi na yaki, wanda ya saba dokokin kasa da kasa, baya ga haka kuma killace yankin a cikin irin wannan yanayi da ake fama da corona, shi ma yana a matsayin wani babban laifi a kan bil adama.

A cikin takardar ta hadin gwiwa, kungiyoyin da kuma cibiyoyin na kasar Norway sun kirayi ministan harkokin wajen kasar da ya matsa lamba a majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar tarayyar turai, domin ganin an matsa lamba kan Isra’ila , da ta kawo karshen killace al’ummar Gaza, wanda kwamitin kare hakkin bil adam na majalisar ya bayyana hakan a matsayin laifin yaki.

 

 

3897299

 

 

captcha