Shafin yada labarai na sabah yaum ya bayar da rahoton cewa, masu adawa da muslunci a kasar Faransa sun yi rubutu na barazanar kisan musulmi a kan bangayen masallaci a garin Cholet a unguwar Favreau.
Masu adawa da muslucni s n yi rubuce-rubuce na batun ga musulmi a kan bangayen masallacin, tare da bayyana cewa za su kashe musulmi masu salla a cikin masallacin.
Abdullahi Zikri daya daga cikin shugabannin musulmi a kasar faransa ya bayyana hakan da cewa lamari ne mai matukar hadari ga rayuwar musulmi mazauan kasar.
Y a ce yana kira ga hukumomin Faransa das u dauki mataki kan wanann lamari tun kafin lokaci ya kure.