IQNA

23:45 - May 24, 2020
Lambar Labari: 3484831
Tehran (IQNA) sojojin Isra’ila sun fada wa wasu Palasdinawa wadanda suke nufin shiga harabar masallacin Al-Aqsa don gudanar da sallar Idi.

Kamfanin dillancin labaran SAFA ya bayar da rahoton cewa, sojojin Isra’ila sun fada wa wasu Palasdinawa waɗanda suke ƙoƙarin shiga harabar masallacin Al-Aqsa don gudanar da sallar Idin karamar salla a yau din nan Lahadi.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin sojojin Isra’ila suna far ma Palasɗinawan a kokarin da suke yi na hana su shiga harabar masallacin mai alfarma da nufin hana su gudanar da sallar Idin, wanda da man tun da fari sun sanya shinge don kare Palasdinawan daga shiga.

Har ila yau wasu rahotannin sun ce sojojin sahyoniyawan ɗauke da makamai sun kai hari kan Palasdinawan a kofar Bab al-Asbat da ke tsohon birnin kudus a ci gaba da takurawa Palasdinawan da suke zaune a birnin.

Daga ƙarshe dai Palasdinawan sun yi salla a wajen harabar masallacin bayan da sojojin suka rufe dukkanin hanyoyi da kofofin shiga Masallacin na aqsa dauke da muggan makamai, a daidai lokacin da ‘yan sanda su ma dauke da makamai suke kewaye su.

A yau ne dai su ma Palasɗinawan kamar sauran ‘yan’uwansu na ƙasashen musulmi suka gudanar da bukukuwan karamar salla don kawo karshen wata guda na azumin watan Ramalana.

 

3901129

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makamai ، lokacin da ، falastinawa ، masallata ، masallacin aqsa ، sallar idi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: