Abdulbasit Muhammad Abdulsamad Salim Dawud, sannnen makarancin kur’ani ne a duniya, wanda ya shahara da kyakkyawan sautinsa na karatun kur’ani, wanda ya kasance shi ne shugaban kungiyar makaranta da mahardata kur’ani na farko a kasar Masar.
An haifi Abdulbasit Abdulsamad a farkon watan Janairun shekara ta 1927 a garin Armenat na kasar Masar, ya kuma rasu a ranar 30 ga watan Nuwamban 1988.
Ya gudanar da karatun surat Waqi’a a kasar Masar a shekara ta 1987, wato shekaru 33 da suka gabata, shekara guda kenan kafin rasuwarsa.