IQNA

Kira Zuwa Ga Haramta Kayan Isra’ila A Ramallah

23:12 - June 25, 2020
Lambar Labari: 3484927
Tehran (IQNA) wasu kungiyoyin farar hula  aFalastinu sun yi kira zuwa ga haramta kayayyakin Isra’ila a garin Ramallah.

Kamfanin dillancin labaran SAFA ya bayar da rahoton cewa, wasu kungiyoyin Falastinawa sun yi kira zuwa ga haramta kayayyakin da Isra’ila take samarwa.

Bayanin kungiyoyin wanda aka fitar a  garin Ramallah, ya  yi kira ga dukaknin falastinawa a duk inda suke a  cikin yankunan Falastinu, da su daina sayen kayayyakin da Isra’ila take samarwa.

Sanarwar ta ce manufar hakan ita ce nuna rashin amincewa da matakan da matakan da Isra’ila take dauka na mamaye yankunan falastinawa, da kuam takura musu a cikin kasarsu, da kuma shirin da take da niyyar aiwatar na mamaye sauran yankunan da suka rage a  hannun Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Kungiyoyin falastinawan sun bayyana shirin na Isra’ila da cewa wani sabon mulkin mallaka ne a kansu, kuma amincewa da shi na a matsayin amincewa da zalunci da danniya a kan al’ummar falastinu.

 

3906787

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :